Koyi Ilimin Taurari, Ramli da Hisabi kyauta.
Wannan sirri ne mai karfi ga mai sana'a ko kasuwanci wanda yake son Allah ya bude masa kofofin arziki. Ana yin sa ne kowace rana bayan an idar da sallar Asuba.
Ma'anar su ita ce "Ya Mai Budawa, Ya Mai Azurtawa". Idan aka lazimci wannan a kowace rana, za a ga abin mamaki wajen samun kwastomomi da albarkar dukiya In Sha Allahu.
Ismullahil A'azam (Sunan Allah Mafi Girma) sirri ne wanda idan aka roki Allah da shi, baya mayar da rokon bawa. Ana amfani da shi wajen wata babbar bukata ko wata matsala mai tsanani da ta ki ci ta ki cinyewa.
يَا حَيُّ يَا قَيُّومُ يَا ذَا الْجَلَالِ وَالْإِكْرَامِ
"Yaa Hayyu Yaa Qayyuum, Yaa Zal Jalaali Wal Ikraam"
Yadda Ake Yi: A tashi a cikin tsakiyar dare (kamar karfe 2:00 na dare), a yi sallah raka'a biyu. Bayan an idar a yi sujjada a karanta wannan sunan kafa 41, sannan a roki bukata kafin a dago kai daga sujjadar. Allah zai biya ba tare da bata lokaci ba.
Ga wanda yake neman farin jini, kwarjini, ko karbuwa a wajen jama'a, ko wajen neman aure, ko wajen neman aiki. Wannan ismun na "Yaa Wadudu" (Mai yawan kauna) sirri ne babba.
Ana karanta "YAA WADUUDU" kafa 400 a kowace rana, musamman bayan sallar Isha'i. Duk wanda ya ganka zai ji yana kaunarka a ransa, kuma zai mutuntaka da izinin Allah.
A duk lokacin da kake jin tsoron makiyan boye, anyi maka jifa, ko ana yawan samun iska da firgita a bacci. Wannan kariya ce mai karfi wadda asiri ko maita ba ya tasiri a kanta.
Wannan garkuwa ce da Annabi (S.A.W) ya koyar da mu. Idan mutum ya lazimci wannan a matsayin addu'ar safe da yamma (Azkar), babu wani jifa ko mugun gani da zai yi masa tasiri In Sha Allahu.
Ga masu fama da matsalolin iska a jiki, ko aljanin dare (mai taushewa ko saduwa da mutum a bacci), ko macen da iska ke hana ta haihuwa. Wannan sirri ne na kona su da fitar da su da izinin Allah.
A rika shafa wannan ruwan a jiki kafin a kwanta bacci, sannan a sha kadan. Haka za'a yi tsawon kwanaki 7. Babu wani aljani da zai iya jure wannan zafin In Sha Allahu.
Suratul Inshirah (Alam Nashraha) sura ce da Allah ya saukar da ita don saukaka musiba da kawar da damuwa. Duk wanda ya rike ta, Allah zai yaye masa kuncin rayuwa ya bude masa kofofin alheri.
Ana karanta "Alam Nashraha laka Sadrak..." gaba dayanta kafa 40 a kowace rana bayan sallar Asuba ko Isha'i.
Faidar Sirrin: Duk wanda ya lazimci wannan adadin (40), koda ba shi da ko taro a aljihunsa, Allah zai kawo masa hanyar arziki ta inda baya tsammani a cikin kankanin lokaci, sannan a wanke masa damuwar ransa gaba daya.
Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce: *"Duk wanda ya karanta Suratul Waqi'ah kowane dare, talauci ba zai taba shafar sa ba."* Wannan sirri ne da manyan malamai da attajirai ke amfani da shi wajen samun dukiya da rufin asiri.
(Ba'a so a karanta ta don jarrabawa, ana son mutum ya karanta da yakinin cewa Allah ne mai azurtawa, kuma zai ga canji mai girma a kasuwancinsa ko aikinsa).
Ga wanda bashi ya yi masa yawa ya rasa yadda zai yi, ko kuma an rike masa hakkinsa ba a so a bashi, wannan addu'ar itace takobin yanke wannan matsalar wadda Manzon Allah (S.A.W) ya koya wa Sayyidina Ali (R.A).
اللَّهُمَّ اكْفِنِي بِحَلَالِكَ عَنْ حَرَامِكَ وَأَغْنِنِي بِفَضْلِكَ عَمَّنْ سِوَاكَ
"Allahummak-finii bi-halaalika 'an haraamika, wa aghninii bi-fadhlika 'amman siwaaka."
"Ya Allah ka isar min da halal dinka daga haramun dinka, ka wadata ni da falalarka daga barin kowa ba kai ba."
Yadda Ake Yi: A lazimci karanta wannan addu'ar kafa 100 a kowace rana bayan sallar Juma'a, ko kuma a rika yinta a cikin sujjada. Ko bashin ya kai girman dutse, Allah zai kawo hanyar biyan sa In Sha Allahu.
Wannan itace addu'ar da Annabi Ibrahim (A.S) ya yi lokacin da za'a jefa shi a wuta, sannan Annabi Muhammad (S.A.W) ya yi ta a yakin Uhud. Makami ne mai ruguza duk wani shiri na makiya ko mahassada.
Idan kana fuskantar babbar barazana, tsoron makiya, ko an shiga hakkin ka, a karanta "HASBUNALLAAHU WA NI'IMAL WAKIIL" kafa 450 a rana. Allah zai kifar da dukkan makircin su ya dawo kan su da izininSa.