Darussan Ramli & Falaki na Malamin Zaure

DARUSSAN MALAMIN ZAURE

🛒 SIYA LITTATTAFAN RAMLI MASU KYAU

Barka da zuwa Sashin Karatu 08109988689

Koyi Ilimin Taurari, Ramli da Hisabi kyauta.

BINCIKE GAME DA BIYAN BUKATA KO WACE IRI

Domin sanin ko bukata zata biya ko wace iri ce, ana daukan Gidan 1 da Gidan 6 a hada su. Tauraron da ya fito daga hadin shine hukunci.

Idan sakamakon ya kasance Nari, sai a duba tauraron da ya zo da Ittisalinsa.

Idan ittisali ya zo da kyau, bukatar zata biya In Sha Allah. Idan babu ittisali ko ya zo da rauni, ana iya samun jinkiri ko cikas a cikar bukatar.

BINCIKE AKAN AURE A RAMLI

Hada Gidan 1 (Ango) da Gidan 7 (Amarya). Sakamako da Gidan 5...

Ranar: 01 Maris, 2026

FITAR DA WANI IRIN JIFA, ISKA DA MAYU A RAMLI

1️⃣ FITAR DA WANI IRIN JIFA NE

1. Kausaji: Anyi jifa ne akan kwabewar al’amuran rayuwa.

2. Rahika: Anyi ne akan toshewar hanyoyin samu da arziki.

3. Nasaratu Kharija: Anyi ne domin a rabaka da wani abu da ka mallaka.

4. Jama’a: Anyi ne domin kore mutum daga cikin mutane ko a bata masa suna.

2️⃣ FITAR DA WANI IRIN ISKA NE

1. Bayadha: Iska ne ta gado (wato daga asali).

2. Dariki: Iska ne wanda aka tsokane shi ko aka taka shi a hanya.

3. Kabla Kharija: Iska ne baki mugu wadda aka turawa mutum.

4. Saa’ili: Iska ne mai shiga jikin mutum son ransa.

3️⃣ FITAR DA WANI IRIN MAYU NE

1. Inkis: Maita ce tsantsa da tsafi.

2. Iskafi: Maita ce ta group (ma’ana suna da yawa).

3. Nasara Dhakila: Maita ce hade da asiri (ma’ana jifa).

4. Nakiyya: Maita ce hade da iskan ture.

Lura: Ilimin Ramli hanya ce ta fahimta da bincike. Allah (S.W.T) shine masani na hakika.

🔥 KA ZAMA KWARARRE A RAMLI DA HISABI 🔥

Kana son ka iya fitar da hukunci da kanka ba tare da tambayar kowa ba? Littattafanmu da Applications dinmu na musamman suna koyar da kai mataki-mataki har ka zama masani.

✅ Littattafan suna dauke da cikakken bayani da misalai a aikace.

✅ Applications dinmu suna bada fassara kai tsaye da kansu.

✅ Ba mu cutar da mutane — ilimi ne domin fahimta da taimako.

✅ Zaka iya gane jifa, iska, mayu da sauran al’amura cikin sauki.

✅ Ko da baka da kwarewa, zaka iya fahimta cikin gajeren lokaci.

Kada ka tsaya a karatu kawai — ka mallaki ilimin gaba daya!

📲 TUNTUBE NI TA WHATSAPP YANZU

Domin samun Littattafai da Applications na Ramli da Hisabi masu bada fassara da kansu.

Ranar: 01 Maris, 2026

BINCIKE WAJAN GANE ME KE DAMUN MARA LAFIYA

Idan ana son a gano me ke damun mara lafiya ta hanyar ilimin Ramli, bayan ka gama yin Turabinka, sai ka dauki wadannan matakai:

Mataki-mataki:

  1. Dauki Gidan Uku (3).
  2. Dauki Gidan Sha-biyar (15).
  3. Hada su waje guda: 3 + 15.
  4. Abin da ya fito (Sakamako), idan ya kasance daya daga cikin taurarin nan, sai a fassara shi kamar haka:

Fassarar Taurari:

🔥 NARI

Idan sakamakon ya kasance Nari, to alamar Jifa ce.

🌬 HAWA'I

Idan ya kasance Hawa’i, daga Allah ne (Jarabawa ko Kaddara).

💧 MA'I

Idan ya kasance Ma’i, alamar Iska ce.

🌍 TURABI

Idan ya kasance Turabi, alamar Mayu ne.

Lura: Allah (S.W.T) shine masani ga dukkan al’amura. Wannan bincike alama ce ta ilimi domin fahimta kawai.

Ranar: 01 Maris, 2026

KARATUN RAMLI AKAN RASHIN LAFIYA: Bayanin Gidaje 16

Lokacin da aka buga kasa domin bincike akan mara lafiya, kowane gida a cikin Ramli yana dauke da sako na musamman dangane da halin da majinyacin yake ciki. Ga fassarar gidajen guda 16 dalla-dalla:

1. Gidan Farko

Yana nuna mara lafiyan da kanshi (Yanayinsa a zahiri).

2. Gidan Biyu

Yana magana akan samun saukin mara lafiya da kuma kashe-kashen kudin da ake yi wajen neman lafiya.

3. Gidan Uku

Yana nuna gudummawa da kulawar da mara lafiya ke samu daga 'yan uwansa da makusanta.

4. Gidan Hudu

Yana bayyana asalin dalilin rashin lafiyar da take damun majinyacin.

5. Gidan Biyar

Yana nuna makwancin majinyaci (Gadon Asibiti/Gida) da kuma irin abincin da yake ci.

6. Gidan Shida

Yana bayyana ainahin ciwon da mara lafiya ke fama da shi.

7. Gidan Bakwai

Yana nuna maganin da mara lafiya ke amfani da shi (Ingancinsa ko rashinsa).

8. Gidan Takwas

Tunanin mara lafiya da nazarinsa akan jinyar: Shin zai tashi ko zai mutu?

9. Gidan Tara

Masu zuwa gaida mara lafiya da kuma irin kulawar (Treatment) da ake masa.

10. Gidan Goma

Likitan da yake wa majinyaci jinya da dukkanin hanyoyin da zai bi wajen magani.

11. Gidan Sha-daya

Zirga-zirga da shige-da-ficen likitoci akan mara lafiya.

12. Gidan Sha-biyu

Barazana akan mara lafiya: Wahalar da zai sha ko kuma saukin da zai samu.

13. Gidan Sha-uku

Nasarar majinyaci akan magungunan da yake sha (Shin suna aiki?).

14. Gidan Sha-hudu

Zaton da mutane suke wa majinyacin: Zai tashi ko ba zai tashi ba?

15. Gidan Sha-biyar

Yana nuna dadewar da mara lafiya zai yi kafin ya samu sauki (tashi).

16. Gidan Sha-shida

Karshen al'amari (Result) da yadda majinyacin zai kasance.

🔥 SO KAKE KA GANO SIRRIN BOYE?

Wannan kadan ne daga cikin ilimin Ramli. Idan kana son zama kwararre, ka iya fitar da hukunci da kanka ba tare da tambaya ba, muna da littattafai da Apps na musamman a gare ka.

"Ilimi shine gishirin rayuwa. Kada ka bari a barka a baya."

SHIGA STORE DOMIN SIYAN LITTATTAFAI
Ranar: 28 Fabrairu, 2026

BINCIKE AKAN AURE A RAMLI: Hanyar Gano Alkhairi

Idan ka zuba kasa domin bincike akan aure, kuma kana so ka gane shin auren zai yiwu? Kuma akwai alkhairi a cikinsa? Ga hanyar da ake bi a ilimin Ramli domin fitar da hukunci tabbatacce.

Yadda Ake Hadawa (Formula):

  • Dauki Gidan 1 (Mai tambaya/Ango).
  • Hada shi da Gidan 7 (Wacce ake so a aura/Amarya).
  • Abin da ya fita (Sakamakon), sai ka hada shi da Gidan 5 (Gidan soyayya, haihuwa, da bushara).

Fassarar Sakamako (Hukunci):

✅ SA'IDI

(Mai Sa'a)

Auren zai yiwu kuma yanada kyau da alkhairi sosai.

⚠️ MUMTAJIZI

(Gauraye/Tsaka-tsaki)

Yana tsaka-tsakiya. Zai iya yiwuwa amma sai an dage da addu'a sosai.

❌ NAHISI

(Maras Kyau)

Bashida kyau kuma bazai yiwu ba. Shawara ita ce a hakura.

Lura: Wannan bincike ne na ilimin taurari don nuna alama, amma Allah (S.W.T) shine masanin gaibu da abin da zai faru gobe.

Ranar: 27 Fabrairu, 2026

YADDA AKE CIRE BURUJI DA MUHIMMANCIN SANIN SA

Muhimmancin Sanin Burujin Mutum

Sanin Burujin mutum ba kawai labari bane, ilimi ne mai zurfi da zai taimaka maka wajen gane kanka da rayuwarka. Shin ka taba tambayar kanka me yasa kake saurin fushi? Ko me yasa wasu ranaku kafi samun sa'a akan wasu? Amsar tana cikin taurarinka.

Ga amfanin sanin Burujinka guda 4:

  • Sanin Addu'ar da ta Dace: Kowani Buruji yana da sunan Allah (Ismul A'azam) da ya fi dacewa da shi. Idan ka san shi, addu'arka tafi saurin karbuwa.
  • Ranar Sa'a: Wasu ranakun mako sun fi dacewa da kai wajen neman kudi ko tafiya. Misali, mai burujin "Sauru" ranar sa'arsa Juma'a ce.
  • Sana'ar da ta Dace: Ba kowace sana'a ce take karbar kowa ba. Wani idan yayi kasuwancin ruwa zai yi asara, amma idan yayi na wuta (kamar walda ko girki) zai yi arziki.
  • Dabi'ar Mutum (Element): Shin kai mai dabi'ar Wuta ne (Nari), ko Kasa (Turabi), ko Iska (Hawa'i), ko Ruwa (Ma'i)? Wannan yana bayyana halayenka na zahiri da boye.

Yadda ake Cire Buruji (Mataki-mataki)

Akwai hanyoyi guda biyu da ake cire buruji. Ta hanyar Suna da kuma ta hanyar Ranar Haihuwa (Date of Birth).

Hanya ta 1: Ta Hanyar Lissafin Suna (Abjad)

Wannan ita ce hanyar da tafi inganci a ilimin Falaki na Musulunci. Ga yadda ake yi:

  1. Dauki adadin sunan mutum (Lissafin Abjad).
  2. Dauki adadin sunan mahaifiyarsa.
  3. Hada su waje guda.
  4. Raba sakamakon da gida 12 (Ko ka ringa cire 12 har ya rage kasa da 12).
  5. Abin da ya rage (Remainder) shine lambar Burujinka.

Misali a Aikace:

Muna so mu cire burujin Sulaiman dan Fadima.

  • 1. Sunan Sulaiman: Adadinshi = 191
  • 2. Sunan Fadima: Adadinshi = 135
  • 3. Jimilla: 191 + 135 = 326
  • 4. Idan aka raba 326 da 12 (ko a cire 12 har ya kare), saura zai zama 2.

Sakamako: Lamba 2 ita ce Burujin SAURU (Taurus).

Dabi'arsa: Turabi (Kasa). Mai hakuri, mai rikon amana, kuma mai son noma ko harkar filaye.

Hanya ta 2: Ta Hanyar Ranar Haihuwa (Date of Birth)

Idan baka san lissafin Abjad ba, zaka iya amfani da watan haihuwarka (Miladiyya):

  • Aries (Hamal): Mar 21 – Apr 19
  • Taurus (Sauru): Apr 20 – May 20
  • Gemini (Jauza): May 21 – Jun 20
  • Cancer (Saratan): Jun 21 – Jul 22
  • Leo (Asad): Jul 23 – Aug 22
  • Virgo (Sunbula): Aug 23 – Sep 22
  • Libra (Mizan): Sep 23 – Oct 22
  • Scorpio (Akrab): Oct 23 – Nov 21
  • Sagittarius (Kaus): Nov 22 – Dec 21
  • Capricorn (Jadi): Dec 22 – Jan 19
  • Aquarius (Dalwu): Jan 20 – Feb 18
  • Pisces (Hutu): Feb 19 – Mar 20

Kana son sanin naka Burujin dalla-dalla?

Malamin Zaure yana nan domin taimaka maka da lissafin cikin sauki.

Tuntube Mu Yanzu
Ranar: 26 Fabrairu, 2026

Tarihin Ilimin Taurari da Gudummawar Musulunci

Gabatarwa:
Ilimin taurari (Astronomy/Astrology) yana daya daga cikin tsoffin ilimomi da dan Adam ya fara sani a doron kasa. Tun kafin zuwan zamani, mutane sun dogara da taurari wajen sanin lokuta, gane alkibla, da kuma fahimtar yanayin duniya. A wannan darasin, zamu duba asalin wannan ilimi da yadda ya zhara a Musulunci.

Asalin Ilimin Tun Farko

Masana tarihi sun bayyana cewa Annabi Idris (A.S) shine mutum na farko da Allah ya sanar da shi ilimin taurari da lissafi. Daga baya, al'ummomi kamar Babiloniyawa (Babylonians) da Masarawa (Egyptians) sun yi fice wajen gina dala da pyramids ta hanyar amfani da lissafin taurari. Sun yi amfani da shi wajen sanin lokacin noma da kuma hasashen abubuwan da zasu faru.

Ilimin Taurari a Musulunci (Falaki)

Musulunci ya bada gudummawa mafi girma a wannan fanni. A lokacin da Turai take cikin duhun jahilci, Malaman Musulunci suna gina "Observatories" (Wuraren kallon taurari). Allah (S.W.T) ya ambaci taurari a wurare da yawa a cikin Al-Qur'ani, yana mai cewa: "Kuma shine wanda ya sanya muku taurari domin ku shiryu da su a cikin duhun tudu da na teku..." (Suratul An'am: 97).

Manyan malamai kamar Al-Khwarizmi (wanda ya kirkiri Algebra/Hisabi) da Al-Biruni sun yi rubuce-rubuce masu yawa. Sun yi amfani da ilimin Falaki wajen:

  • Gane Alkiblar Sallah daga ko ina a duniya.
  • Sanin lokutan Sallah guda biyar.
  • Gane shiga da fitar watannin Musulunci (Ramadan da Hajji).

Bambancin Falaki da Ramli

Yana da kyau mai karatu ya gane bambanci. Falaki ilimi ne na lissafin motsin taurari a sararin samaniya (Astronomy). Shi kuma Ramli, ilimi ne na buga kasa ko lissafin yadda taurari ke shafar dabi'un dan Adam (Geomancy/Astrology).

A nan gidan Malamin Zaure, muna koyar da duka bangarorin biyu bisa tsari na ilimi da bincike, domin taimakawa al'umma wajen sanin taurarinsu, dabi'unsu, da kuma magungunan da suka dace da su.

Ranar: 20 Fabrairu, 2026

Misalin Lissafin Falaki: Umar da Khadija

Domin gano tauraron mutum, muna amfani da lissafin sunansa da na mahaifiyarsa. Ga misali a kasa:

Sunan Umar (عمر): Jimilla = 310

Sunan Khadija (خديجة): Jimilla = 622

Jimillar Gaba Daya: 932

Idan aka raba 932 da gida 12, saura za ta zama 8.

Sakamakon lissafin ya nuna cewa tauraron wannan bawan Allah shi ne BURUJIN AKRABU (Scorpio). Wannan yana nuna dabi'unsa na zurfin tunani da jarumta.

Gabatarwa: KARIJAI

Ana kiran wadannan taurarin KARIJAI. Wace hanya ka sani da za'a ringa ganesu cikin sauki? RAHIKA, KABLA KARIJA, NASARA KARIJA, SA'ILI.

YADDA AKE CIRE BURUJI

Sanin buruji yana taimaka wajen sanin sana'a da ranar sa'a...

Siya Littafin Lissafi
⬅ Baya 9 10 11 Gaba ➡