Darussan Ramli & Falaki na Malamin Zaure

DARUSSAN MALAMIN ZAURE

🛒 SIYA LITTATTAFAN RAMLI MASU KYAU

Barka da zuwa Sashin Karatu 08109988689

Koyi Ilimin Taurari, Ramli da Hisabi kyauta.

Koma Jerin Darussa
Binciken Marar Lafiya
Darasi na 23 Ilimin Ramli / Bincike

Bincike Game Da Marar Lafiya 🩺

Bayanin Gidaje 16 Akan Marar Lafiya

Idan aka zuba kasa domin duba marar lafiya, ga abin da kowane gida a cikin gidaje 16 yake fassarawa game da shi:

1. Gidan Farko: Yana nuna marar lafiyan kansa.
2. Gidan Biyu: Yana magana akan samun saukin marar lafiya da kashe-kashen kudin da ake yi domin samun saukin majinyaci.
3. Gidan Uku: Yana nuna gudumawa da marar lafiya ke samu da kulawa wajan 'yan uwansa.
4. Gidan Hudu: Dalilin rashin lafiyan ne a kan majinyaci.
5. Gidan Biyar: Makwancin majinyaci ne da abincin da yake ci.
6. Gidan Shida: Ciwon da marar lafiya ke fama da shi.
7. Gidan Bakwai: Magani da mara lafiya ke amfani da shi.
8. Gidan Takwas: Tunanin marar lafiya ne, da nazarinsa kan jinyansa; zai tashi ko zai mutu.
9. Gidan Tara: Masu zuwa gaishe da mara lafiya ne, da treatment da ake wa majinyaci.
10. Gidan Goma: Likitan (Doctor) da yake wa majinyaci jinya da dukkanin treatment da zai yi masa.
11. Gidan Sha Daya: Zirga-zirga da shige da fice na likitoci akan marar lafiya.
12. Gidan Sha Biyu: Barazana ce akan marar lafiya na wahala da zai sha ko saukin da zai samu.
13. Gidan Sha Uku: Nasaran majinyaci ne akan magungunan da yake yi.
14. Gidan Sha Hudu: Zato da mutane suke wa majinyaci ne, zai tashi ko ba zai tashi ba.
15. Gidan Sha Biyar: Yana nuna adewa da marar lafiya zai yi kafin ya tashi.
16. Gidan Sha Shida: Yana nuna karshen al'amari da majinyaci zai kasance.

1. Bincike Wajan Gane Meke Damun Marar Lafiya

Bayan ka yi turabinka, zaka hada gidan uku da gidan sha biyar, ma'ana 3 + 15. Dan da ya baka in ya kasance daya daga cikin taurarin nan, ga abin da yake nufi:

  • 🔥 In Nari Ne: Jifa ne.
  • 💨 In Hawa'i Ne: Daga Allah ne.
  • 💧 In Ma'i Ne: Iska ne.
  • 🌍 In Turabi Ne: Mayu ne.

2. Fitar Da Wani Irin Jifa Ne (Nari)

  • 1. Kausaji: An yi jifan ne akan kwabewan al'amuran rayuwa.
  • 2. Rahika: An yi akan toshewan hanyoyin samu.
  • 3. Nasaratu Kharija: An yi akan a raba ka da wani abu da ka mallaka.
  • 4. Jama'a: Domin kore ma mutane da sauransu.

3. Fitar Da Wani Irin Iska Ne (Ma'i)

  • 1. Bayadha: Iska ne ta gado.
  • 2. Dariki: Iska ne wanda aka tsokane shi ko aka taka shi a hanya.
  • 3. Kabla Kharija: Iska ne baki mugu wadda aka tura wa mutum.
  • 4. Sa'ili: Iska ne mai shiga jikin mutum son ransa.

4. Fitar Da Wani Irin Mayu Ne (Turabi)

  • 1. Inkis: Maita ne tsantsa da tsafi.
  • 2. Iskafi: Maita ne na group, ma'ana suna da yawa.
  • 3. Nasara Dakhila: Maita ne hade da asiri, ma'ana jifa.
  • 4. Nakiyya: Maita ne hade da iskan ture.
Baya Gaba