Sirruka 4 Masu Girma Daga Taskar Malamin Zaure 🌿
Wannan wata tsaraba ce ta musamman daga taskar mu ga dukkan masu bibiyar wannan shafi. Idan mutum ya rike wadannan sirrukan da yakini, zai ga abin mamaki in sha Allah.
1. Sirrin Neman Budin Kasuwa a Wajan Allah
Duk wanda kasuwancinsa ya tsaya, ko yake neman abin dogaro da kai, ya lazimci karanta wadannan Sunayen Allah:
"YAA RAZZAAQU, YAA FATTAAHU"
Adadi: Kafa 308 kowace rana bayan sallar Asuba.
Sharadi: Idan za a fara, a yi Istigfari (100), da Salatin Annabi (100). Ana cikin yin wannan, Allah zai bude kofofin arziki ta inda ba a zata ba.
2. Sirrin Farin Jini da Karbuwa
Wanda yake son kowa ya so shi, a rika jin maganarsa a cikin jama'a, ko wanda sana'arsa take bukatar mutane (Kamar dillanci ko siyasa):
A karanta "YAA WADUUDU" kafa 20 a kan ruwan sha da sassafe kafin a yi magana da kowa, sannan a sha ruwan a shafa a fuska. Haka za a rika yi tsawon kwanaki 7. Kowa ya gan ka zai ji ka burge shi a ransa.
3. Sirrin Neman Tsari Daga Asiri da Makiya
Domin karya asirin makiya da samun kariya daga idon mutane, ka lizimci karanta Ayar nan:
"Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakiil"
Adadi: Kafa 450 a daren kowace Alhamis ko Lahadi. Wallahi duk wanda ya kulla maka sharri sai ya koma kansa, kuma babu abin da zai same ka da izinin Allah.
4. Sirrin Maganin Gargajiya (Itatuwa)
Maganin Wanke Ciki, Basir, da Karfafa Garkuwar Jiki: Wannan wani hadin itatuwa ne mai matukar tasiri wanda yake fitar da datti a ciki, ya magance basir mai turo dubura ko mai sa zafin jiki.
- Garin Habbatus-Sauda (Cokali 2)
- Garin Tafarnuwa (Cokali 1)
- Zuma Farar Saka (Cokali 5)
Yadda ake amfani da shi: A kwaba su waje daya su hadu sosai. A rika shan cokali daya da sassafe kafin a ci komai, da kuma cokali daya da daddare idan za a kwanta. Yana sa a yi bayan-gida mai kyau, ya kashe tsutsar ciki, sannan ya kara wa mutum lafiya sosai.