Darussan Ramli & Falaki na Malamin Zaure

DARUSSAN MALAMIN ZAURE

🛒 SIYA LITTATTAFAN RAMLI MASU KYAU

Barka da zuwa Sashin Karatu 08109988689

Koyi Ilimin Taurari, Ramli da Hisabi kyauta.

40. BINCIKE GAME DA WAYE YAI JIFA

Ana daukan Gidan 6 da 12. Abinda ya fita ma shine siffar wanda yai jifan, imma namiji ko mace.

41. BINCIKE GAME DA RUWAN SAMA

Ana duba Gidan 5. Tauraron da aka samu:
🔥 Nari: Za’ai hadari sosai.
🌬 Hawa’i: Za’ai iska sosai.
💧 Ma’i: Kamar za’ai ruwa ko ya iyafi.
🌍 Turabi: Garanti za’ai ruwa In Sha Allah.

42. BINCIKE GAME DA CIWON H.I.V

Ana duba Gidan 6. In an samu Qabla Kharija ko Nari ko Hawa’i, akwai haka. In aka bugi tauraron da ya sauka a gidan da mai gidan, dan in Dhakili ne, akwai In Sha Allah.

43. BINCIKE GAME DA RABO (HAIHUWA)

Ana daukan Gidan 1 da 5 dan ka hadashi da 15. Abinda ya baka in Jama’a ne, za’a samu rabo. Haka tauraron in Ma’i ko Turabi, to akwai haihuwa. Tsabanin haka babu.

44. BINCIKE GAME DA ARZIKI

Ana hada Gidan 2 da 11 dan a hadashi da 15. Abinda ya baka:
✅ Sa’idi: Zai yi arziki.
❌ Nahisi: Ba zai yi ba.
⚠️ Mumtajizi: Shi ba talaka ba, ba mai kudi ba.

45. BINCIKE GAME DA KARSHEN ZAMANKU

Ana daukan Gidan 3 da 7 dan a hadashi da 16. Tauraron da ya baka:
🤝 Sa’idi: Za’a rabu lafiya.
😡 Nahisi: Za’a rabu da fushi.
😐 Mumtajizi: Za’a rabu ba da shiri ba.

46. BINCIKE GAME DA AL'ADA (HAILA)

Ana daukan Gidan 6 da 7. Dan da ya bayar:
🔒 Ma’inshi a kulle: Batayi.
🔓 Ma’inshi a bude: Tana al’ada In Sha Allahu.

47. BINCIKE GAME DA KARBAR ADDU'A

Ana daukan 7 da 8. Dan da ya baka:
🚪 Sa’idi Khariji: Addu’a ya karbo.
🏠 Sa’idi Dhakili: A kara addu’a.
🚫 Tsabanin haka: A chanza aikin da ake yi.

48. BINCIKE GAME DA WARKEWA

Ana daukan Gidan 4 da 6, sai Gidan 5 da 8. Dan in Sa’idi ne Dhakili, ya warke. In Sa’idi Khariji, yana kan samun sauki In Sha Allahu.

49. BINCIKE GAME DA MUTUM YANA GIDA

Ana duba Gidan 14. Dan da ka samu in Dhakili ne, yana gida. Tsabanin haka, ba ya nan In Sha Allahu.

Baya Gaba