Koyi Ilimin Taurari, Ramli da Hisabi kyauta.
Ana daukan tauraron da ya sauka a Gidan 8, sai ka bugeshi. Dan da ya baka:
🔓 Hawa’inshi a bude: Yana son ya baka.
🔒 Hawa’inshi a kulle: Ba ya son bayarwa.
Ana duba Gidan 1, da Gidan 7, da kuma Gidan 3. Idan aka samu sa’idan taurari a gidajen, to aure yana da kyau In Sha Allah.
Ana daukan Gidan 1 da Gidan 4 a hada su. Idan sa’idi ne, ya dace ka aureta ko ki aureshi. Idan nahisi ne, bai dace ba In Sha Allah.
Ana daukan Gidan 7 da Gidan 10 a hada su. Idan sa’idi ne, akwai ci da sha In Sha Allah.
Ana daukan Gidan 1 da Gidan 11, sannan a dauki Gidan 8 da Gidan 12. Sai a hada sakamakon duka biyun.
Ana duba Gidan 1, da Gidan 7, da kuma Gidan 11. Idan aka samu sa’idan taurari wato masu kyau, harkar tana da alkhairi. Idan ba haka ba, babu In Sha Allah.
Domin sanin wa yafi son ɗan’uwansa a tsakanin masoya, ana yin bincike ta hanyar lura da wuraren da suke a cikin qasa.
Wanda ya zo wajenka domin tambaya yana wakiltar Gidan 7. Wanda ake tambaya akansa yana wakiltar Gidan 14.
A duba taurarin da suka fito a wadannan gidaje. Duk tauraron da yafi Sa’idi wato wanda yafi kyau da karfi, shi ne yake nuna wanda yafi son ɗan’uwansa In Sha Allah.