Darussan Ramli & Falaki na Malamin Zaure

DARUSSAN MALAMIN ZAURE

๐Ÿ›’ SIYA LITTATTAFAN RAMLI MASU KYAU

Barka da zuwa Sashin Karatu 08109988689

Koyi Ilimin Taurari, Ramli da Hisabi kyauta.

30. BINCIKE GAME DA YAWAN FADA DA ABOKIN ZAMA

Ana daukan Gidan 6 da 12. Dan da aka samu:
โœ… Saโ€™idi ne: Daga Allah ne.
โŒ Nahisi ne: Jifa ne.
โš ๏ธ Mumtajizi ne: An jefesu da Iska ne.

31. BINCIKE GAME DA MUTUM YANA DA KUDI

Ana daukan Narin daya, Hawaโ€™in biyu, Maโ€™in uku, Turabin hudu a maida shi tauraro sai a bugeshi da Gidan 2. Abinda aka samu:
๐Ÿ’ฐ 2, 4, 12, 15: Yana da kudi masu yawa.
๐Ÿ’ต 6, 7, 8, 9: Yana da kudi amma basu da yawa.
๐Ÿšซ Tsabanin haka: Babu In Sha Allah.

32. BINCIKE GAME DA KUDIN KYAUTA KO BASHI

Ana daukan 1 da 7 dan a hadashi da 2, dan a hadashi da 11. Abinda ya bayar in Saโ€™idi ne Dhakili, sannan ya zo da Ittisalinshi, za'a samu a lokacin da izinin Allah.

33. BINCIKE GAME DA MAI LAIFI ZAI DAINA

Ana bin Lamiri inda ya kare ma. Sai kaga wane tauraro ne:
โœ… In Khariji ne: Ya daina.
โŒ In Dhakili ne: Bai daina ba In Sha Allah.

34. BINCIKE GAME DA ADADIN BARAYI

Ana duba Gidan 7. Tauraron da ka samu, adadin Mai-Maituwansa shine adadin barayin In Sha Allah.

35. BINCIKE GAME DA MARA LAFIYA ZAI WARKE

Ana duba Gidan 6. In ya zo da Imfisalinshi a kasan, zai warke In Sha Allahu.

36. BINCIKE GAME DA FADAN MIJI DA MATA

Ana daukan 1 da 7 dan a hadashi da 15. Abinda aka samu:
โœ… Saโ€™idi ne: Daga Allah ne.
โŒ Nahisi ne: Jifa ne.
โš ๏ธ Mumtajizi ne: Iska ne In Sha Allah.

37. BINCIKE GAME DA MUTUM YANA RAYE

Ana daukan Gidan 1 da 8 dan a hadashi da 15. Abinda ya baka in ya zo kasan, yana raye. Tsabanin haka kuma ya mutu In Sha Allahu.

38. BINCIKE GAME DA MATAFIYI ZAI DAWO

Ana duba Gidan 7 da 9. In an samu Saโ€™idan taurari, zai dawo In Sha Allahu.

39. BINCIKE GAME DA MAI NASARA

Ana daukan Gidan 13 da 16 dan a hadashi da 10. Abinda ya bayar:
๐Ÿ  Dhakili ne: Mai tambaya ne da nasara.
๐Ÿšช Khariji ne: Wanda ake tambaya ne da nasara.
๐Ÿšซ Munqalabi ko Sabiti: Dukansu basu da nasara.

Baya Gaba