Koyi Ilimin Taurari, Ramli da Hisabi kyauta.
Ana daukan gidan 1 da 7 dan abugeshi da gidan 4 danda yabayar in dhakiline ko sabiti to dan garine sabanin haka mutun cirani yazo in sha allahu.
Ana daukan gidan 1 da 16 dan ahadashi da 15 abinda akasamu in sa’idine dhakili to ayi abun akwai alkhairi in sha allahu.
Ana daukan narin nari, ma’ana zaka dau unsutin nari na kowane gidan nari. Sune gidan 1 da 5 da 9 da 13. To tauraronda yabaka in sa’idi ne sannan yazo da ittisalinshi a kasan, to tafiyan akwai alkairi in sha allahu.
Ana daukan gidan 9 da 15. Dan da aka samu idan dhakili ne, a siya. Sabanin haka, a barshi In Sha Allahu.
Ana daukan gidan 1 da 5 da kuma gidan 3 da 11. Dan da aka samu in dhakili ne, zasu kai. Idan kuma ba dhakili bane, ba zasu kai soyayyarsu dakin aure ba, In Sha Allahu.
Ana daukan Gidan 2 da 11. Dan da ya baka in ya zo a 1 ko 2, za’a samu. In baka samu hakan ba, to ka dubi tauraron: in Sa’idi ne sannan Ma’inshi a bude, za’a samu da izinin Allah.
Ana duba Gidan 10. In an ga daya daga cikin taurarin nan, to zargi ya tabbata. In ba’a gani ba, a nemesu a kasan gaba daya.
Ana duba Gidan 6. In an samu wadannan taurari, zargi ya tabbata:
Ana duban Gidan 7 da 9. Tauraron da aka samu in Sa’idi ne, tafiyar nada kyau. In sun saba, ka haifesu; dan da ka samu in Sa’idi ne, tafiyar tana da kyau In Sha Allah.